Isa ga babban shafi
Coronavirus-Najeriya

Gwamnati ta baiwa mazauna Abuja da Legas shawarar zama a gida

Gwamnatin Najeriya ta baiwa mazauna biranen Legas da Abuja shawarar cewar kowa ya zauna a gidansa sakamakon samun karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus wadda ta kai ga mutuwar mutum guda.

Wani mai saye da mai sayarwa a kasuwar dake birnin Legas a Najeriya. 5/3/2020.
Wani mai saye da mai sayarwa a kasuwar dake birnin Legas a Najeriya. 5/3/2020. REUTERS/Temilade Adelaja
Talla

Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya Boss Mustapha dake jagorancin kwamitin yaki da cutar ne ya bada wannan shawara, tare da haramta duk wasu tarurrukan jama’a har sai abinda hali yayi nan gaba.

Ya zuwa yanzu an tabbatar da samun mutane 42 da suka kamu da cutar, mutum guda ya mutu, yayin da 2 suka warke.

A Kaduna dake arewacin Najeriya, Gwamnan Jihar Malam Nasir El Rufai ya bayyana daukar matakai na neman kariya da kuma dakile yiwuwar yaduwar annobar murar ta COVID-19 ciki harda haramta tarukan ibada a Masallatai Da Mujami’u, wadda yace tuni aka baiwa jami’an tsaro umarnin tabbatar da soma aikin dokar.

01:09

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i kan matakan dakile annobar Coronavirus

Nura Ado Suleiman

Matakan Gwamnatin Kaduna na zuwa ne yayinda ministan sadarwa a Najeriyar Lai Mohammad, ya gargadi al’ummar kasar su kasance cikin shirin ko-ta-kwana saboda nan ba da jimawa ba Gwamnati na iya sanya umarni mai tsauri a matsayin wani mataki na dakile yaduwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.