Isa ga babban shafi
Coronavirus

Gwaji ya nuna Kyari ya kamu da coronavirus

Rahotanni daga Najeriya kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito na cewa shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin kasar Abba Kyari ya kamu da cutar coronavirus, bayan gwajin lafiyarsa da cibiyar bincike da dakile yaduwar cutuka ta NCDC tayi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati Abba Kyari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati Abba Kyari. Sahara Reporters
Talla

Sai dai gwaje-gwajen jami'an lafiyar ya nuna cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari baya dauke da cutar kamar yadda akewa duk wanda aka gano makusancinsa na dauke da ita.

Jaridun Thisday da kuma 'Premium Times dake Najeriyar sun ce wasu majiyoyin fadar gwamnatin kasar da suka nemi a sakaya su ne suka tabbatar da labarin.

Har zuwa lokacin wallafa wannan labarin dai gwamnati bata tabbatar da rahoton ba a hukumance, zalika babu wanda ya musanta lamarin.

Bayanai sun ce a yanzu za a gudanar da gwaje-gwajen kamuwa da cutar ta coronavirus kan makusantan Abba Kyari, da kuma wadanda ya gaisa da su a baya bayan nan, ciki har da tsohon sakataren gwamnatin Najeriya Babagana Kingibe, sai kuma hamshakin attajirin nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote, da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, da kuma babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu.

Rahotanni sun ce yanzu haka wadanda ke aiki tare shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Najeriyar da dama sun killace kansu.

A ranar 7 ga watan Maris shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Najeriyar Abba Kyari ya ziyarci Jamus tsawon mako daya, wanna tasa ake zargin cewar ya kamu da cutar ce a kasar ta Jamus, daya daga cikin kasashen Turan da annobar murar ta coronavirus ta yiwa illa.

Wannan na zuwa a dai dai lokacin da ma’aikatar lafiyar Najeriya ta tabbatar da karuwar adadin wadanda suka kamu da cutar murar a fadin kasar zuwa 40, 28 a birnin Legas, daga cikin mutanen kuma 2 sun warke guda ya mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.