Isa ga babban shafi
Najeriya

Legas ta sa ido kan baki sama da 300 saboda Coronavirus

Gwamnatin Legas a Najeriya, ta ce yanzu haka tana sa idanu kan akalla mutane 349 da suka yi tattaki zuwa jihar daga kasashe daban daban, saboda cutar Coronavirus.

Wani jami'in lafiya yayin bincike kan kwayoyin cuta.
Wani jami'in lafiya yayin bincike kan kwayoyin cuta. Wera Rodsawang/Getty Images
Talla

Ma'aikatar lafiyar jihar ta Legas ta ce baki dayan mutanen dake karkashin sa idon sun fito ne daga kasashen da annobar murar ta Coronavirus ta yi karfi.

Cibiyar lura da dakile yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, ta ce tana bukatar naira biliyan 1 da miliyan 600 don yakar annobar murar ta Corona, daga ciki kuma kawo yanzu gwamnatin tarayyar kasar ta mika mata naira miliyan 984.

Yanzu haka dai bayaga Najeriya, kasashen Afrika da suka tabbatar da bullar annobar murar cikinsu sun hadada Masar, Algeria, Afrika ta Kudu, Senegal, Kamaru, da kuma Togo. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.