Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta killace karin mutane saboda annobar Coronavirus

Hukumomin Najeriya na cigaba da sanya ido kan mutane da dama sakamakon barazanar kamuwa da cutar coronavirus wadda aka tabbatar cewar ta shiga kasar makon jiya.

Wasu jami'an lafiya a Najeriya bayan tabbatar da rahoton bullar annobar Coronavirus a kasar.
Wasu jami'an lafiya a Najeriya bayan tabbatar da rahoton bullar annobar Coronavirus a kasar. Quartz
Talla

La'akari da cewa karin haske kan yanayi da kuma alamun kamuwa da cutar ta Coronavirus yana da muhimmancin kwarai, sashin Hausa na RFI ya tuntubi  babban Sakataren kula da lafiya na Gwamnatin Najeriya Abdulaziz Abdullahi Mashi, wanda yayi bayani kan alamun cutar da kuma matakin da ya dace a dauka.

00:49

Najeriya ta killace karin mutane saboda annobar Coronavirus

Nura Ado Suleiman

Kwamishinan lafiyar Jihar Lagos inda aka samu cutar, Akin Abayomi yace akwai mutane da dama da aka killace kuma ake cigaba da dubar lafiyar su, duk da yake yaki bayyana adadin su.

Abayomi ya kuma bayyana cewar ana cigaba da kula da lafiyar dan kasar Italian da ya shiga kasar da cutar, yayin da manyan jami’an kula da lafiya na gwamnatin Tarayya suka isa Lagos domin taimaka musu.

Bayan Lagos an kuma killace mutane a Jihohin Ogun da Plateau da aka bayana cewar ana zargin sun kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.