Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumar INEC ta soke jam'iyyun siyasa 74 a Najeriya

Hukumar Zaben Najeriya Mai Zaman Kanta, INEC ta soke rajistar jam’iyyun siyasar kasar har guda 74, abin da ke nufin cewa, jam’iyyu 18 kacal suka tsallake shirinta na rage yawan jam’iyyu a kasar.

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya, Farfesa Yakubu Mahmood
Shugaban Hukumar Zaben Najeriya, Farfesa Yakubu Mahmood News Express Nigeria
Talla

Wannan na zuwa ne bayan Hukumar ta INEC ta yi nazari tare da tantance rawar da jam’iyyun siyasar suka taka bayan kammala zabukan 2019 , inda ta gano jam’iyyun da suka cancanci ci gaba da wanzuwa.

Fitattu daga cikin jam'iyyun siyasar da aka soke har da jam'iyyar National Conscience Party, NCP wadda marigayi Gani Fawehinmi, fitaccen lauya a Najeriya ya kafa, sai kuma Peoples Coalition Party wadda ta yi ta uku a zaben shugaban kasa na bara, sai kuma KOWA Party da Fresh Democratic Party da tsayar da Rev. Chris Okotie a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa na 2006.

A lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a birnin Abuja, shugaban INEC, Frafesa Mahmod Yakubu ya ce,  hukumar ta tsayar da ranar 19 ga watan Satumban shekarar 2020 a matsayin ranar gudanar da zaben gwamnan jihar Edo da kuma ranar 10 ga watan Oktoba a matsayin ranar gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.