Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya na neman dala biliyan 62 daga manyan kamfanonin hakar mai

Najeriya ta soma yunkurin karbar kudaden da adadinsu ya kai dala biliyan 62, daga wasu manyan kamfanonin hakar mai dake kasar, kudaden da ta ce ya kamata kamfanonin su biya ta a tsawon shekaru 20 da suka gabata.

Najeriya tayi ikirarin bin manyan kamfanonin hakar mai bashin dala biliyan 62.
Najeriya tayi ikirarin bin manyan kamfanonin hakar mai bashin dala biliyan 62. AFP Photo/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

A shekarar 1993, dokar da gwamnatin Najeriyar ta kafa kan sa ido bisa aikin hakar danyen man da kasafta ribarsa ta fayyace cewar, kamfanonin za su kara adadin kudaden harajin da suka biyan kasar, idan farashin gangar danyen man ya zarta dala 20.

Bayan soma aikin dokar a waccan lokacin, kamfanonin hakar man sun amince da biyan kashi 20 na ribar da suke samu duk shekara ga Najeriya.

Sai dai duk da cewar farashin gangar danyen man ya daga sosai cikin sama da shekaru 20 da suka gabata, ba a waiwayi dokar sabunta harajin da ya kamata kamfanonin su rika biyan gwamnatin Najeriyar ba. Wannan ce ta sa a yanzu, kasar ta ce lokaci yayi da kamfanonin za su cika tsohuwar yarjejeniyar da ta cimma da su, ta hanyar biyan basukan harajin da basu saka a lalitar ta ba, da adadinsu ya kai dala biliyan 62.

Sai dai da alama manyan kamfanonin hakar man basu amince da ikirarin gwamnatin Najeriyar ba, domin kuwa tuni suka daukaka kara kan batun.

Kamfanonin da Najeriya ke neman hakkin nata na ribardala biliyan 62, sun hada da Equinor (Norvège), Esso (Exxon Mobil), CNOOC (China) da kuma Shell.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.