Isa ga babban shafi
Najeriya

Attajiran Najeriya sun yiwa tawagar Super Eagles alkawarin kudade

Manyan Attajiran Najeriya guda biyu, Aliko Dangote da Femi Otedola sun yiwa Yan wasan tawagar Super Eagles na Najeriya dake gasar cin kofin Afirka a Masar alkawarin kudade idan sun samu nasara a sauran wasannin su guda biyu da suka rage, bayan nasarar da suka samu a wasan daf da na kusa da na karshe kan Afirka ta kudu.

Cocin tawagar 'yan wasan Nageriya Super Eagles Gernot Rohr da wasu 'yan wasa
Cocin tawagar 'yan wasan Nageriya Super Eagles Gernot Rohr da wasu 'yan wasa Reuters
Talla

Yayin ziyarar da suka kaiwa kungiyar a otel din da suke a Birnin Alkahahira, Aliko Dangote yayi alkawarin biyan Dala 50,000 kan kowanne kwallo guda da kungiyar ta jefa a wasannin da za suyi nan gaba, yayin da Femi Otedola yayi alkawarin Dala 25,000 kan kowanne kwallo guda.

Kafin wannan alkawarin, wani attajirin Najeriya mai harkar mai, Captain Hosea Wells Okunbo ya yiwa kowanne dan wasa guda alkawarin Dala 20,000 idan sun doke kamaru kuma ya biya su bayan nasara da suka samu, kana shima Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu ya baiwa kowanne Dan wasa Dala 5,000 saboda gagarumar nasara da suka samu akan Kamaru.

Ita ma kamfanin man AITEO dake hadin gwuiwa da Hukumar kwallon kafar Najeriya ta biya Dala 25,000 akan kowanne kwallo guda da Najeriya ta jefa a wasan Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.