Isa ga babban shafi
Najeriya

Kano: Sarki Sunusi ya gana da Ganduje a Abuja

Gwamnatin Kano ta hannun sakataren yada labaranta Abba Anwar, tabbatar da cewa an samu ganawa tsakanin gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje da kuma Mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II, a daren Juma’ar da ta gabata a garin Abuja.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma Mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma Mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II. Solacebase
Talla

Sanarwar ta ce, ganawar sulhunta tsamin dangantakar shugabannin 2, ta gudana ne a karkashin jagorancin attajiri Aliko Dangote, da kuma shugaban gwamnonin Najeriya dakta Kayode Fayemi.

Dagantaka tsakanin shugabannin ta soma yin tsami ne, yayin yakin neman zabukan da suka suka gabata a farkon wannan shekara ta 2019, inda bangaren gwamnati ke zargin Sarkin Kano da fifita wani bangare.

Daga bisani dai gwamnatin ta Kano ta dauki matakin daga matsayin wasu masarautun jihar guda 4 zuwa masu daraja ta 1, abinda ke nufin kasafta masarautar Kano zuwa kashi 5.

Masarautun da aka daga darajarsu kuwa sun hada da Gaya, Karaye, Bichi da kuma Rano. Gwamnatin ta kare matakin da cewa ta zartas da shi ne da kyakkyawar manufa, ba don kuntatawa Sarki Muhammadu Sunusi na II ba da nufin rage karfin ikonsa, kamar yadda da dama ke zargi.

A baya bayan nan ne kuma gwamnatin Kano ta bukaci Sarki Muhammadu Sunusi na II, da ya kare kansa, daga zargin fadarsa da barnatar da kudaden tafiyar da masarauta, da adadinsu ya zarta naira biliyan 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.