Isa ga babban shafi
Najeriya

Tsokaci kan rantsuwar wasu gwamnonin jihohi a Najeriya

Gwamnoni 29 ne suka yi rantsuwar kama aiki jiya Laraba a Najeriya, wasu a karo na biyu wasu kuma a karo na farko.

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, yayin rantsuwar kama aiki.
Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, yayin rantsuwar kama aiki. YouTube
Talla

Daga cikin jimillar gwamnonin 29 da aka rantsar, 12 sabbi ne da ke kama aiki, yayin da 17 sun samu nasarar lashe zabe ne a karo na biyu.

Gwamnonin, masu kama wa’adin aiki na biyu da na farko sun dauki alkawurra da dama da suka ta’allaka ga samar da ribar dimokaradiyya, yayin da wasu daga cikinsu suka soma da warware wasu shirye-shirye da suka gada daga gwamnoni masu barin gado.

Sabon gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya soke wasu kwangiloli da karin girma da aka yiwa ma’aikata a baya bayan nan, zalika gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya da ya kama aiki a karon farko shi ma irin matakan ya dauka.

Gwamnan jihar Kano kuwa, da ya samu damar yin wa’adi na biyu da jibin goshi, Abdullahi Umar Gaduje yayi alkawarin bayar da ilimi kyauta yayin bikin rantsar da shi, wanda sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu bai samu halarta ba.

A jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya, sabon gwamna, Seyi Makinde na kammala yin rantsuwa, ya kada baki ya ce jihar, ba za ta iya biyan sabon mafi karancin albashin ma’aikata ban a naira dubu 30, yana mai cewa gwamnatin tarayya ba ta yi adalci ba wajen sanya hannu a dokar da ta shafi sabon albashin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.