Isa ga babban shafi
Najeriya

An samar da dokar kisa kan masu sace jama'a a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, Aminu Masari ya sanya hannu kan dokar Penal Code da aka yi kwaskwarima wadda kuma ta bayyana satar jama’a da shanu a matsayin manyan laifukan da suka cancanci hukuncin kisa.

Gwaman Jihar Katsina, Aminu Masari ya koka kan tabarbarewar tsaro a jihar
Gwaman Jihar Katsina, Aminu Masari ya koka kan tabarbarewar tsaro a jihar Dandago
Talla

Dokar ta kuma amince da hukuncin daurin rai da rai ga masu yi wa mata fyade.

A yayin gabatar da jawabi, Gwamna Masari ya ce, jihar Katsina na fama da matsalar tsaro, abinda ya sa aka yi wa dokokin jihar gyarar fuska.

Kazalika Gwamnan ya bayyana fatan cewa, matakin da suka dauka a yanzu, zai tsawatar da mutanen da ke da shawa’ar shiga harkar sace-sacen jama’a domin karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.