Isa ga babban shafi
Najeriya

Al'ummar Batsari sun jibge gawarwakin jama'arsu a fadar Sarki

‘Yan bindiga sun kashe akalla mutane 20 a wasu hare-haren da suka kai jihar Katsina da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya kamar yadda jami’an ‘yan sanda suka tabbatar, yayinda mazauna yankin suka jibge gawarwakin mutanen a fadar Sarkin Katsina da kuma gidan gwamnati domin tabbatar wa hukumomi irin ibtila'in da suke gani a kowacce rana.

'Yan bindiga sun kashe mutane 20 a jihar Katsina
'Yan bindiga sun kashe mutane 20 a jihar Katsina Information Nigeria
Talla

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah ya bayyana cewa, ‘yan bindigan akan babura sun yi ruwan harsashai kan mai uwa da wabi a kauyen Yargamji da ke yankin Batsari mai tazarar kilomita 50 daga babban birnin Katsina.

Rahotanni sun ce, mayakan sa kai ne suka yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar, inda suka bi su har cikin daji domin dauki ba dadi.

Wasu daga cikin mayakan na sa kai sun gamu da ajalinsu a yayin musayar wuta da maharan kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Jihar Katsina na fama da tashe-tashen hankula a ‘yan watannin nan, yayinda kuma ake sace jama’a domin karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.