Isa ga babban shafi
Najeriya

Matasan Zamfara sun kashe 'yan bindiga a fadar sarki

Wasu matasan Karamar Hukumar Birnin Magaji da ke jihar Zamfara a Najeriya, sun yi wa fadar sarkin yankin kawanya, in da suka kashe ‘yan bidiga 7 da suka halarci fadar sarkin da nufin tattaunawar zaman lafiya.

Matasan Zamfara sun kashe 'yan bindiga bakwai a kusa da fadar sarkin Birnin Magaji
Matasan Zamfara sun kashe 'yan bindiga bakwai a kusa da fadar sarkin Birnin Magaji Dailytimes
Talla

Rahotanni sun ce, ‘yan bindigar sun halarci fadar ne domin tattaunawar zaman lafiyar bayan jami’an tsaro sun kwace shanunsu a hare-haren saman da jami’an suka kai kan sansaninsu da ke dajin Birnin Magaji.

Hare-haren sojin saman Najeriya sun tarwatsa ‘yan bindigar, yayinda wasu daga cikinsu suka koma cikin gari domin ci gaba da rayuwa a bainal jama’a, lamarin da ya jefa tsoro a zukutan al'umma.

Kazalika hare-haren sun tilasta wa ‘yan bindigar barin shanunsu da yawansu ya kai 200, kuma tuni sojoji suka kwashe shanun, in da aka boye su a fadar sarkin Birnin Magaji kafin daga bisani a tasa keyarsu zuwa birnin Gusau a makon jiya.

A jiya Laraba ne, ‘yan bindigar suka ziyarci fadar sarkin domin ganin sun yi sulhun da zai kai ga mika musu shanunsu.

Sai dai tuni matasan yankin suka yi wa fadar kawanya tare da kokarin kona fadar sarkin, lamarin da ya sa sojoji suka lallashe su.

Matasan sun far wa ‘yan bindigar ne bayan sun fito daga fadar sarkin, kuma nan take suka aika su lahira.

Rahotanni sun ce, sarkin na Birnin Magaji na ziyara a jihar Kaduna lokacin da wannan al’amari ya faru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.