Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Najeriya ta samu Onnoghen da laifin almundahana

Kotun Ladabtar da Ma’aikata ta Najeriya ta samu tsohon babban mai shari’a na kasar, Walter Onnoghen da laifin almundahana, in da ta haramta masa rike duk wani mukami har na tsawon shekaru 10.

Walter Onnoghen a tsakiya a gaban zauren Kotun Kula da Da'ar Ma'aikata ta Najeriya a Abuja
Walter Onnoghen a tsakiya a gaban zauren Kotun Kula da Da'ar Ma'aikata ta Najeriya a Abuja Reuters/ Stringer
Talla

Hukuncin Kotun karkashin Danladi Umar na zuwa bayan zargin da aka yi wa Onnoghen na bayar da bayanan karya da kuma boye kadarorinsa.

Kotun ta kwace kudaden da Onnoghen ya mallaka a wasu asusun bankuna biyar domin mika su ga gwamnatin tarayyar Najeriya bayan hujjoji sun nuna cewa, tsohon babban mai shari’ar ya mallake su ne ta hanyar da baa dace ba, sannan kuma ya gaza gabatar da hujja kan yadda ya same su.

Kotun ta yi amfani da sashi na 23 na kundin dokokin da’ar ma’aikata da ya ba ta karfin tsige Onnoghen daga kujerarsa.

Kodayake makwanni da suka gabata, Mr. Onnoghen ya aike wa shugaban kasar Muhammadu Buhari da wasikarsa ta murabus bayan shawarwarin da Hukumar Kula da Shari’a ta bayar.

Sai dai kawo yanzu, shugaba Buhari bai yi karin bayani ba game da ajiye aikin Onnoghen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.