Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ce ta 6 wajen shan wahala a duniya

Wani rahoto daga jami’ar John Hopkins da ke Baltimore ta Amurka, ya bayyana Najeriya a matsayin ta 6 a jerin kasashen da suka fi fama da kuncin rayuwa a duk fadin duniya.

Birnin Legas na Najeriya cike da hada-hadar jama'a da ababan hawa
Birnin Legas na Najeriya cike da hada-hadar jama'a da ababan hawa ©Reuters/Greg Ewing
Talla

Rahoton wanda wani masanin tattalin arziki, Steve Hanke ya rubata kuma aka wallafa a Mujallar Forbes, ya ce, an yi amfani da mizanin tattalin arziki da rashin aikin yi da tsadar kayayyakin masarufi da kuma kudin ruwa da bankuna ke karba, wajen ayyana kasashen da suka fi fama da kuncin rayuwar.

Matsalar rashin aikin yi na kan gaba wajen jefa al’ummar Najeriya cikin kuncin rayuwa kamar yadda rahoton ya bayyana.

Rashin aikin ne ya sa Najeriya ta makale a matsayi na shida a jerin kasashen na duniya, in ji rahoton.

Venezuela ce ke kan gaba wajen kuncin rayuwar, sai Argentina da aka bayyana a matsayi na biyu, Iran ta uku, Brazil ta hudu, Turkiya ta biyar, sai Najeriya a matsayi na shida.

Kasashen Thailand da Hungary aka bayyana a matsayin kasashen da ke kan gaba wajen samun sassaucin kuncin rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.