Isa ga babban shafi
Najeriya

Zaben Najeriya: "Rana ba ta Karya"

'Yan Najeriya na kada kuri’a a manyan zabukan kasar, inda aka soma da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na zauren dattijai da kuma wakilai.

Wasu masu kada kuri'a a zabukan shugaban Najeriya da na 'yan majalisun tarayya a birnin Legas.
Wasu masu kada kuri'a a zabukan shugaban Najeriya da na 'yan majalisun tarayya a birnin Legas. RFIHAUSA
Talla

Zabukan sun zo ne a dai dai lokacin da ‘yan Najeriya suka zaku wajen ganin sun jefawa’yan takarar da suke so kuri’a, biyo bayan sauya ranakun zabukan da karin wa’adin kwanaki 7 da hukumar INEC ta yi.

A makon da ya gabata, hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, ta bayyana dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun wakilai da dattijai saboda matsalar isar da kayayyaki zabe da kuma gobarar da ta tashi a wasu ofisoshinta, inda shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu y ace babu Siyasa ko kadan cikin batun dage zaben.

A waccan lokacin Farfesan yasanarda sauya ranar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisunsa na tarayya daga 16 na Fabarairu zuwa yau 23 ga watan, yayinda zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun dokoki aka sauya ranar da zai gudana daga 2 zuwa 9 ga watan Maris.

Yayin da yake Karin bayani kan halin da hukumar ta INEC ke ciki a jiya Juma’a, shugaban na ta Farfesa Mahmood Yakubu, ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewar sun kammala dukkanin shirye-shiryen da suka dace domin ganin zabukan sun gudana kamar yadda aka tsara, inda y ace tuni kayan aiki suka isa baki dayan kananan hukumomin Najeriya 774 da ke sassan kasar.

Farfesa Yakubu ya kara da cewa, hukumar ta kammala shirin amfani da ababen hawa da suka hada da motoci da Babura dubu 80, da za a yi amfani da su wajen jigilar ma’aikatanta dubu 825 da 543, sai kuma jiragen ruwa 996 da za su yi jigilar ma’aikatan da kayan aiki, zuwa yankuna masu ruwa da ke bukatar hakan.

A cewar shugaban na INEC, hukumar ta tantance kungiyoyin sa ido kan zabukan Najeriyar 120 na cikin gida, yayinda ta tantance 36 daga kasashen ketare, a jimlace kuma yawan jami’ai masu sa’ido kan zabukan ya kai dubu 73.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.