Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya yi jawabi kan zaben Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummar kasar da sauran masu sa ido na ciki da waje da su yi amanna da Hukumar INEC da za ta gudanar da zaben shugabancin kasar a gobe Asabar ba tare da matsala ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP
Talla

A yayin gabatar da jawabin da aka watsa kai tsaye a gidajen rediyo da talabijin na kasar a safiyar yau Jumm’a, shugaba Buhari ya ce, ya yi amanna cewa, Hukumar INEC ta dauki darasi daga kura-kuran da ta tafka a baya, kuma a yanzu ta shirya gudanar da zabukan kasar.

A bangare guda, shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da suka mallaki katunan kada kuri’u da su fita rumfunar zabe domin fayyace makomar kasar.

"Ina bukatar ku fita domin kada kuri’unku " In ji Buhari.

Sama da mutane miliyan 70 ne suka karbi katunansu domin kada kuri’a a zaben shugabancin kasar da na ‘yan majalisar tarayya a Najeriya, in da shugaba Buhari na Jam’iyyar APC zai fafata da Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP.

A makon jiya aka shirya gudanar da zaben amma aka dage shi bayan Hukumar Zaben Mai Zaman Kanta INEC, ta ce, ta gamu da matsalar isar da kayayyakin zabe a wasu wurare.

Sai a wannan karo, INEC ta ce, ta shirya domin gudanar da zaben a gobe Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.