Boko Haram ta kai sabon hari a Rann
Wasu da ake zatan mayakan Boko Haram ne, sun kashe mutane akalla 10 tare da kona gidaje da dama a wani hari da suka kaddamar a garin Rann da ke karamar hukumar Kala-Balge da ke jihar Bornon Najeriya.
Wallafawa ranar:
Majiyoyi sun rawaito cewa, mutane da dama sun jikkata a farmakin wanda aka kai cikin daren da ya gabata.
Maharan sun isa garin ne cikin ayari, in da kuma suka far wa sansanin soji, yayin da rahotanni ke cewa, an kwashe tsawon sa'o'i ana musayar wuta tsakanin sojin da mayakan.
Majiyoyin sun ce, mayakan sun fatattaki sojojin saboda irin manyan makaman da suke dauke da su.
Hare-haren Boko Haram sun kazanta a ‘yan kwanakin nan, al'amarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji suka janye ma’aikatansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu