Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya ta lallasa Libya a gasar kwallon yashi

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles mai wakiltarta a gasar kwallon yashi ta nahiyar Afrika, ko kwallon bakin teku dake gudana a Masar, ta samu nasarar farko bayan soma gasar.

Najeriya ta lallasa Libya da kwallaye 6-3 a gasar kwallon yashi.
Najeriya ta lallasa Libya da kwallaye 6-3 a gasar kwallon yashi. Yahoo
Talla

Najeriya wadda ke rukunin B, ta lallasa kasar Libya da kwallaye 6-3 a wasan da suka fafata na ranar Lahadi.

A wasan farko dai Super Eagles din na kwallon kafar yashi, sun yi rashin nasara ne da kwallaye 2-0 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, a hannun takwarorinsu na Senegal masu rike da kofin gasar, bayan tashi wasan farkon da suka fafata 4-4.

Su kuwa Libya sun lallasa Tanzania da kwallaye 5-0 ne a wasan farkon.

A yau Litinin Najeriya za ta fafata wasan karshe na rukuni da Tanzania, wadda a jiya Lahadi ta sha kashi a hannun Senegal da kwallaye 12-2.

Kasar da ta lashe kofin gasar kwallon yashin da kuma ta biyu ne za su wakilci nahiyar Afrika a gasar kwallon yashin ta duniya da kasar Paraguay za ta karbi bakunci a sabuwar shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.