Isa ga babban shafi
Najeriya

An sake yin arrangama tsakanin 'yan Shi'a da Sojoji a Abuja

Rahotanni daga Najeriya sun ce an sake samun arangama tsakanin mabiya akidar Shi’a da jami’an tsaro, bayan wanda aka samu a karshen mako.

Wasu jami'an sojin Najeriya yayin kokarin hana mabiya akidar Shi'a shiga cikin garin Abuja domin gudanar zanga-zanga. (29/10/2018)
Wasu jami'an sojin Najeriya yayin kokarin hana mabiya akidar Shi'a shiga cikin garin Abuja domin gudanar zanga-zanga. (29/10/2018) REUTERS
Talla

Arrangamar ta auku ne a Nyanya dake babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Jami’an tsaro sun zargi mabiya kungiyar da kai hari kan jami’an su ta hanyar jifa da duwatsu da wasu abubuwan da za a iya amfani da su a matsayin makami, zalika sojin Najeriyar, sun kuma zargi mabiya Shi’ar da kokarin kwace bindiga, yayin da kungiyar tayi watsi da zargin.

Rahotanni sun ce rikicin ya soma ne, bayan da wasu jami’an soji suka hana wata tawagar mabiya akidar ta Shi’a isa inda za su gudanar da zanga-zangar neman a saki shugabansu El-Zakzakky, wanda aka kama a shekarar 2015, biyo bayan arrangamar da mabiyan nasa suka yi da tawagar sojin Najeriya da babban Hafsansu Lafatanar Janar Tukur Buratai ke ciki, a garin Zaria dake Kaduna.

Mai Magana da yawun kungiyar Ibrahim Musa, ya zargi jami’an tsaro da kai hari da kuma kashe magoya bayan su ba tare da dalili ba, yayin da ya ce babu wani daga cikin su dake dauke da makami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.