Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya kadu da gobarar kasuwar Jos

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa al’ummar jihar Filato kan mummunar gobarar da ta lakume shaguna sama da 200 a kasuwar Terminus da ke birnin Jos, in da ya ce, ya kadu da wannan ibtila'in.

Kasuwar Terminus da ke garin Jos a Filato
Kasuwar Terminus da ke garin Jos a Filato rfihausa
Talla

Wata sanarwa da mai taimaka wa Buhari kan harkokin watsa labarai, Garba Shehu  ya fitar ta ce, shugaba Buhari ya ce, ya kadu matuka da wannan ibtila’in da ya haddasa asarar dukiya mai tarin yawa.

Buhari ya kuma nuna damuwa kan cewa, a karo na uku kenan cikin shekaru 10 da irin wannan gobara ke barna a wannan kasuwa.

Shugaban ya kuma bukaci hukumomin da ke da ruwa da tsaki da su dauki matakan da suka dace wajen hana yawaitar aukuwar gobarar.

A yayin zantawa da sashen hausa na RFI, shugaban 'yan kasuwar Alh. Mustapha Ibrahim Bako ya ce, yanzu haka suna kan gudanar da bincike don gano musabbabin tashin gobarar wadda ta fara tun da misalin karfe 1 na dare a ranar Jumma’a.

01:14

Muryar shugaban 'yan kasuwar Terminus da ta kone

Alh. Mustafa ya ce, ba a samu asarar rai a ibtila’in ba, amma dukiyar da ta salwanta na da matukar yawa, kuma suna ci gaba da tattara alkaluma don sanin kudaden da aka yi asarar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.