Masallata sun tsallake rijiya da baya a Yobe
Masu ibada a wani Masallaci da ke kauyen Gashua a karamar hukumar Gujba a jihar Yobe ta Najeriya sun tsallake rijiya da baya, bayan samun nasarar dakile yunkurin da wata mata ta yi na tarwatsa bama-baman da ta yi damara da su a jikinta.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahotanni na cewa, matar ta keta matakan tsaron da aka tanada don kutsawa cikin Masallacin, amma mambobin ‘yan kato da gora suka hange ta tare da dakatar da ita a lokacin da take dawainiya da jikidar bama-baman.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa, matar ta yi niyar tayar da bama-baman ne a daidai lokacin da ake shirin fara salla a cikin Masallacin da ke kauyan Gujba a karamar hukumar Gashua.
Tuni dai aka mika matar da ake kyautata zaton alakarta da Boko Haram ga jami’an tsaro don ci gaba da gudanar da bincike.
Ko da yake an ce, a halin yanzu matar na samun kulawa a wani asibiti sakamakon raunin da ta samu a yayin hana ta tayar da bama-baman.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu