Allah Ya yi wa Isyaka Rabi'u rasuwa a birnin London
Rahotanni daga jihar Kano da ke arewacin Najeriya na cewar babban malamin addinin Musulunci kuma shugaban Darikar Tijjaniya na Afrika Sheikh Isyaka Rabi'u ya rasu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shahararren malamin ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin London, in da ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya kamar yadda iyalansa suka shaida wa manema labarai a yau da magariba.
Maraigayi Sheikh Isyaka Rabiu wanda aka haifa a shekara ta 1928 ya rasu yana da shekaru 90 a duniya.
Ko da yake kawo yanzu babu cikakken bayani game da jana'izar marigayin wanda aka sani da yi wa addinin musulunci hidima.
Daga cikin 'ya'yan marigayin akwai Alhaji Abdus-samad, shugaban kamfanin BUA da kuma Alhaji Karami, shugaban kamfanin jiragen sama na IRS.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu