Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta soke sauye-sauyen majalisun Najeriya kan tsarin zabuka

Kotu a birnin Abuja da ke tarayyar Najeriya ta soke sauye-sauyen da majalisun kasar suka yi wa dokar zabe wadda matukar aka amince da ita za a gudanar da zaben gwamnonin jihohi ne kafin na shugaban kasa.

Zauren majalisar wakilan Najeriya.
Zauren majalisar wakilan Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A watan Fabarairun da ya gabata, majalisun Najeriya suka amince da kudurin sauya tsarin zabukan kasar na shekarar 2019.

Yayin yanke hukuncin, mai shara’a Ahmed Muhammad ya yi nuni da cewa hukumar shirya zaben Najeriya, INEC ce ke da ikon tsarawa da kuma sanya lokutan gudanar da zabukan kasar, kamar yadda kundin tsarin mulki ya fayyace, amma ba majalisa ba.

Mai shara’a Muhammad, ya kara da cewa, yunkurin majalisun Najeriyar, ya sabawa kundin tsari mulki, zalika majalisun sun yi kutse cikin aikin da nasu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.