Isa ga babban shafi
Najeriya-Lafiya

Najeriya ta ki amincewa da masarar da aka sauyawa halitta

Gwamnatin Najeriya ta bada umurnin mayar da wata masara ton 90, da aka sauyawa kwayar halitta bayan an shiga da ita kasar ba tare da izini ba.

Misalin daya daga cikin masarar da aka sauya ko kuma inganta kwayar halittarta.
Misalin daya daga cikin masarar da aka sauya ko kuma inganta kwayar halittarta. REUTERS/Vincent Kessler
Talla

Darakta Janar na Hukumar kula da ingancin abinci, Rufus Egbegba, ya shaidawa manema labarai cewa, sakamakon bayanan da suka samu, hukumar sa ta bada umurnin fitar da masarar daga cikin Najeriya saboda saba ka’ida.

Daraktan yace kafin daukar matakin sai da suka gudanar da binciken kimiya kan masarar har sau 6, domin kare lafiyar jama’a.

Bayanai sun ce Hukumar Kwastam ce ta kama masarar da aka shigar da ita cikin kasar daga Argentina, wadda kudinta ya kai dala miliyan 10 a tashar jiragen ruwan Apapa da ke jihar Legas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.