Isa ga babban shafi
Najeriya

Kwastam ta gano buhunan shinkafar roba a Najeriya

Jami’an hukumar Kwastam ta Najeriya sun gano buhunan shinkafar roba mai lahani ga lafiyar jama'a da aka shigo da su cikin kasar.

An shigo da shinkafar roba a Najeriya
An shigo da shinkafar roba a Najeriya
Talla

Babban jami'in hukumar mai kula da shiya ta farko a jihar Legas, Haruna Mamudu ya shaida wa manema labarai cewa, sun kwace buhuna 102 na shinkafar da aka adana a dakin ajiye kayayaki da ke Ikeja.

Jami’in ya kara da cewa, an shirya siyar da shinkafar ce a daidai lokacin bikin Kirismeti, kuma babu cikakken bayani game da kamfanin da ya sarrafa shinkafar.

Kazalika ba a rubuta ranar da shinkafar ta fito ba, da kuma ranar da za ta lalace, kamar yadda ake gani a sauran buhuna na kayan abinci.

Hukumar kwastam din dai na ci gaba da bincike don gano sauran wuraren da aka adana shinkafar mai suna BEST TOMATO, tare da hukunta masu shigo da ita daga kasashen waje.

Shinkafar dai na haifar da cutar da ke sanadiyar mutuwar jama'a kamar yadda kwararru a fannin kiwon lafiya suka sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.