Isa ga babban shafi
Najeriya

Birtaniya na horar da sojin Najeriya 28,000 don yakar Boko Haram

Birtaniya na duba yiyuwar saidawa Najeriya kayyakin soji domin yaki da kungiyar Boko Haram kamar yadda Boris Johnson, Sakataren harkokin wajen Birtaniya ya bayyana a ziyar da ya ke yi a birnin Legas.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson.
Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson. Reuters Africa
Talla

Mr. Johnson ya shaida wa manema labarai cewa, a halin yanzu, akwai sojojin Najeriya dubu 28 da ke samun horo daga Birtaniya don tinkarar mayakan na Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya, in da matsalar ta fi kamari.

A dai cikin wannan watan na Agusta ne ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ta sanar majalisar kasar shirinta na sai dawa gwamnatin Najeriya jiragen yaki kirar Super Tucano A-29 da kuma wasu makaman da kudinsu ya kai dala miliyan $593 domin murkushe mayakan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.