Isa ga babban shafi
Najeriya

Kashi 95 na al'ummar Najeriya na karbar cin hanci

Wani rahotan bincike mai tada hankali ya nuna cewar kashi 95 na al’ummar Najeriya na mu’amala da cin hanci da rashawa ta hanyar bayarwa ko kuma karba.

Matsalar cin hanci ta tsananta a Najeriya kamar yadda hukumar kididdiga ta kasar ta sanar
Matsalar cin hanci ta tsananta a Najeriya kamar yadda hukumar kididdiga ta kasar ta sanar REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Rahotan wanda hukumar kididdigar kasar ta fitar ya ce, kashi 5 ne kadai na 'yan Najeriya ke kin karba ko kuma bada cin hanci idan an bukaci haka daga gare su.

Hukumar ta ce, a shekara guda akan bada cin hancin da ya kai Naira biliyan 400, kuma kashi 90 na cin hancin ana bai wa jami’an gwamnati ne domin neman biyan wata bukata.

Rahotan ya ce,  a cikin watanni 12 ire-iren wadannan jami’an gwamnati sun karbi kudin da ya kai Naira biliyan 400 a matsayin cin hanci.

Wandai na dada nuna yadda matsar cin hanci da rashawa ta samu gindin zama a Najeriya, abin da a mai yawan lokaci ke cutar da rayuwar al'umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.