Isa ga babban shafi
Najeriya

Dattawan Borno sun bukaci sulhu da Boko Haram

Kungiyar Dattawan jihar Borno ta Najeriya da ta kunshi tsoffin sojoji da fararen hula, ta bukaci gwamnatin kasar da ta yi zaman sulhu da mayakan Boko Haram da zimmar kawo karshen zub da jini na tsawon shekaru takwas.

Hare-haren Boko Haram na neman sake kazanta a 'yan kwanakin nan
Hare-haren Boko Haram na neman sake kazanta a 'yan kwanakin nan HO / BOKO HARAM AFP / AFP
Talla

Cikin wata sanarwa da ta fitar, Kungiyar Dattawan ta Kanuri ta ce, a can baya, gwamnatin Najeriya ta samu nasara a tattaunar sulhun da ta yi da mayakan Niger Delta, abin da ya sa ta ke ganin gwamnatin za ta iya samun nasara a tattaunawa da Boko Haram.

Kungiyar ta ce, lokaci ya yi da ya kamata mayakan Boko Haram su ajiye makamanta, sannan kuma su tuba daga ayyukansu don ci gaba da rayuwa a cikin jama’a.

Kawo yanzu dai, babu wata alama da ke nuna cewa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na shirin tattaunawar sulhu da mayakan.

Kazalika hare-haren Boko Haram na neman sake kazanta a ‘yan kwanakin nan tun bayan tafiyar shugaba Buhari birnin London don duba lafiyarsa, domin ko a jiya Litinin sai da mutane akalla 8 suka rasa rayukansu a wani kunar bakin wake a Masallacin Maiduguri.

Shugaban Chadi Idris Deby ya ce, rashin lafiyar Buhari ta haifar mu su da cikas a yakin da su ke yi da Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.