Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Farashin kayan masarufi ya fara sauka

Hukumar Kididdigar Najeriya, ta ce watanni Uku kenan a jere, kasar na samun cigaba a fanin tattalin arziki, da a baya ya fuskanci babban koma baya da ya haifar da haw-hawar farashin kayan masarufi.

Nijeriya: farashin kayayyakin masarufi ya fara sauka.
Nijeriya: farashin kayayyakin masarufi ya fara sauka. financialtribune
Talla

Ministar kudin kasar Kemi Adeosun ta sakamakon na bayyana cewa ‘yan Najeriya na daf da darawa, sakamakon fitar da kasar zata yi daga matsalar komadar tattalin arziki irinsa mafi muni da ta taba fuskanta a tsawon shekaru.

A lokacin da yake fashin baki kan wannan sabon rahoton, yayin zantawarsa da sashin hausa na RFI, Dakta Issa Abdullahi masanin tattalin arziki a Najeriya, da ke sashin nazarin kimiyyar siyasa a jami’ar Kashere da ke jihar Gombe, yace cigaban alama ce da ke nuna cewa kwalliya ta fara biyan kudin sabulu dangane da tsare tsaren gwamnatin Najeriya da aiwatar don farfado da tattalin arzikin kasar.

Dakta Abdullahi ya kuma danganta samun nasarar da dagawar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya, wanda har yanzu yak e da tasiri kan tattaliln arzikin Najeriya.

To sai dai yayinda hukumomi, masana tattalin arziki da ma sauran mutane ke murnar samun wannan sauki, a gefe guda da dama daga cikin al’ummar Najeriya na kokawa kan yadda har yanzu basu fara ganin tasirin farfadowar tattalin arzikin ba, ta hanyar saukar farashin kayan masarufi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.