Isa ga babban shafi
Najeriya

Bamu da hannu wajen kai samame gidan Goje - EFCC

Hukumar yaki da cin hanci rashawa ta Najeriya EFCC, ta ce babu hannun jami’anta wajen kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Gombe, kuma dan majalisar dattijai a yanzu, Danjuma Goje, da ke garin Abuja.

Tambarin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC.
Tambarin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC. RFI / Pierre Moussart
Talla

Kakakin hukumar ta EFCC Wilson Uwajeren ya bayyana haka, cikin wata takardar sanarwa da ya fitar, inda ya ce babu hannun hukumar cikin samamen da aka kai don bincika gidan tsohon Gwamnan.

Wata majiyar tsaro ta shaidawa jaridar Premium Times da ake wallafawa a Najeriya cewa, jami’an tsaron da suka kai samamen sun fito ne daga wani sashi na ofishin Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya.

Majiyar ta yi karin hasken cewa jami’an sun samu bayanan sirri ne dake cewa akwai makudan kudaden da ke boye a gidan tsohon Gwamnan, wadanda ake zargin anyi sama da fadi ne da su.

Har yanzu dai hukumar ‘yan sandan Najeriya bat ace komai ba dangane da batun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.