Isa ga babban shafi
Najeriya

Arik ya soke zuwa London da kuma Johannesburg

Hukumar Najeriya da ta karbe ragamar tafiyar da kamfanin jiragen Arik ta sanar da soke zirga zirga tsakanin Najeriya da London da kuma Johannesburg.

AMCON ta kwace ragamar tafiyar da Kamfanin jiragen Arik da ke neman durkushewa
AMCON ta kwace ragamar tafiyar da Kamfanin jiragen Arik da ke neman durkushewa
Talla

Mai Magana da yawun hukumar, Jude Nwauzor, ya ce an dauki matakin ne dan gyara da kuma tabbatar da biyan bukatar zirga zirgar cikin gida.

Jami’in ya ce suna ci gaba da tattaunawa da masu bin kamfanin bashi wanda hankalin su ya tashi kan halin da kamfanin ke ciki.

Nwauzor ya ce duk wani fasinja da ya biya kudin tafiya wadannan kasashe biyu za’a mayar masa da kudin sa.

Gwanatin Najeriya ta karbe ragamar tafiyar da kamfanin Arik ne sakamakon neman durkushewa saboda tarin bashin da ake bin sa, duk da dai kamfanin ya ce zai kalubalanci wannan matsayi a Kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.