Ma'aikatan kwadago na yajin aiki a Arik Air
Kungiyoyin kwadago da ke bangaren sufurin jiragen sama sun yi barazanar durkusar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Arik daga yau Talata saboda abin da suka kira kasa biyan albashin watanni 7 da kuma dawo da ma’aikatan da aka kora daga aiki.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da shugabanin kungiyoyin suka gabatar, cikin su har da matuka jiragen da injiniyoyi, ta nuna cewar yajin aikin nasu zai ci gaba har illa Masha-Allahu, matukar kamfanin bai biya hakkokin ma'aikatan ba.
Yajin aikin ba karamar illa zai yi wa matafiya a Najeriya ba, musamman a wannan lokaci na tafiya hutu, ganin cewar kamfanin ne mafi girma a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu