Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Dattawan Najeriya ta tsige Ndume

Mambobin Majalisar Dattawan Najeriya karkashin jam’iyyar APC mai mulkin kasar sun tsige Ali Ndume daga mukaminsa na shugaban gungun masu rinjaye a majalisar.

Ali Ndume
Ali Ndume premiumtimesng.com
Talla

Shugaban Majalisar Dattawan ne Sanata Bukola Saraki ya karanta wasikar da jiga-jigan APC suka aiko masa da ke kunshe da bayanin tsige Ndume.

Wasikar ta bayyana Ahmed Lawan daga jihar Yobe a matsayin wanda zai maye gurbin Ndume kamar yadda Saraki ya karanta.

A lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, Mr. Ndume ya bayyana kaduwarsa da matakin jiga-jigan APC na sauke shi daga kujerarsa, yayin da ya ce ba shi da masaniya game da makasudin tsige shi .

Sai dai ana zaton matakin tsigewar nada nasaba da zargin cin rashawa da ake yi wa Sakataren gwamnatin kasar Babachir Lawal da kuma kin tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, wato EFCC.

Ana saran majalisar za ta tabbatar da nadin Ahmed Lawan a matsayin sabon shugaban gungun masu rinjayen a zamanta na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.