Isa ga babban shafi
Najeriya-Chibok

Gwamnatin Najeriya ta musanta sake sako 'yan matan Chibok

Gwamnatin Najeriya tace tana ci gaba da tattaunawa don ganin ta karbo sauran ‘yan matan Chibok sama da 200 da kungiyar Boko Haram tayi garkuwa da su sama da shekaru biyu.

'Yan matan makarantar Chibok da Boko Haram suka yi garkuwa da su
'Yan matan makarantar Chibok da Boko Haram suka yi garkuwa da su
Talla

Mai Magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ya bayyana haka, yayinda yake musanta wasu rahotanni da ke cewa an saki wasu yam matan jiya.

Garba Shehu yace har yanzu ana ci gaba da tattaunawa tsakanin hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya da kuma wakilan kungiyar ta Boko Haram domin sakin karin matan.

A cikin wannan shekarar kungiyar ta saki ‘yan matan 21 sakamakon irin wannan tattaunawar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.