Isa ga babban shafi
Najeriya

Za'a gudanar da zabe a Jihar Ondo kamar yadda aka tsara

Hukumar Zabe a Najeriya tace ba zata dage zaben Gwamnan Jihar Ondo da aka shirya yi a karshen wannan mako ba, kamar yadda wasu jam’iyyun siyasa suka bukata.

Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu
Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu
Talla

Shugaban Hukumar Mahmood Yakub wanda ke ganawa da masu ruwa da tsaki a zaben na Ondo, yace halin da ake ciki a Jihar bai bada damar dage zaben ba.

Jam’iyyar PDP da wasu jam’iyyu 16 ne suka bukaci hukumar ta dage zaben saboda kararakin dake kotuna dangane da tsayar da dan takara.

Zalika sun kuma bayyana fargabar kan yiwuwar barkewar rikicin siyasa a kasar muddin aka gudanar da zaben kamar yadda aka tsara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.