Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumar zaben Najeriya bata cimma matsaya ba kan dage zabe a Edo

Hukumar kula da shirya zabe a Najeriya INEC ta ce har yanzu bata cimma matsaya ba, dangane da shawarar dage zaben Gwamna a jihar Edo da hukumomin tsaron kasar suka bata.

Talla

Kakakin hukumar ta INEC Nick Dazang ya ce jami'an gudanarwar hukumar suna tattaunawa a taron masu ruwa da tsaki da ke gudana a garin Benin kafin sanar da shawarar da hukumar zata yanke kan batun.

A jiya laraba ne hukumar ‘yansandan Najeriyar da kuma hukumar binciken sirri ta DSS suka bawa hukumar INEC din shawarar dage zaben saboda yiwuwar samun barazanar tsaro yayin zaben.

Hukumomin tsaron dai sun ce akwai yiwuwar samun barazanar tsaro yayin bukukuwan Sallah a ranakun 12 da 13 ga watan Satumba da muke ciki, kuma jihar Edo da ake shirin kada kuri’ar zaben gwamna na daga cikin jihohin ake shirin kaiwa harin.

Dangane da haka babban sakataren gudanarwa na kungiyar Jama’atu Nasril Islam da ke da babban ofishinta a jihar Kaduna Dr Khalid Abubakar Aliyu shawarci mutane su kara himma wajen bawa jami'an tsaro hadin kai domin gudanar da aikinsu cikin nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.