Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumar Custom ta kori jami'anta 29 a Najeriya

Hukumar hana fasa kauri ta Najeriya wato Custom ta sallami manyan jami’anta 29 bayan ta same su da aika manyan laifuka.

Shugaban hukumar hana fasa kauri wato Custom ta Najeriya, Kanar Hamid Ali mai ritaya
Shugaban hukumar hana fasa kauri wato Custom ta Najeriya, Kanar Hamid Ali mai ritaya hopefornigeriaonline.com
Talla

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a wanann Alhamis ta ce, mutanen na cikin jami’anta 44 da ta hukunta saboda aikata wasu laifuka da ke barazana ga sha’anin tsaro da kuma tattalin arzikin kasar.

A makon jiya ne, hukumar ta kori jami’anta guda 17 saboda samun su da laifukan da ke da nasaba da karban cin hanci da ta’ammuli da miyagun kwayoyi da kuma amfani da takardun shaidan karatu na jabu har ma da rashin halartar wurin aiki.

Tun bayan nadin Kanar Hamid Ali mai ritaya a matsayin shugaban hukumar, ya bayyana cewa, hukumar ba za ta amince da cin hanci da rashawa da kuma munanan dabi’u tsakanin jami’anta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.