Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Najeriya mazauna Amurka zasu habaka tattalin arzikin kasar

‘Yan Najeriya mazauna kasar Amurka sun ce a shirye suke su zuba jari domin habaka tattalin arzikin kasar muddin gwamnati zata samar da kaykkyawan tsarin da zai basu damar yin hakan.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da wasu 'yan Najeriya mazauna kasar Amurka
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da wasu 'yan Najeriya mazauna kasar Amurka
Talla

'Yan Najeriyar sun bada wannan tabbaci a lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake ganawa da su a birnin New York a yau Juma’a.

Taron dai ya maida hankali kan tattauna yadda kwararrun ‘yan Najeriyar zasu bada gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

An dai gudanar da wannan taro a daidai lokacin da ake taron Majalisar Dinkin Duniya kashi na 71 a birnin na New York da ke Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.