Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnati ta yi watsi da shawarar karin farashin mai

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da shawarar tsoffin shugabanin kamfanin man kasar na kara farashin mai saboda abinda suka kira hauhawar farashin Dala da ake sayo man da su.

Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Hukumar kayyade farashin mai tace gwamnati bata da niyyar amincewa da wanna bukata saboda ganin halin da talakan Najeriya ke ciki.

Tsoffin ma'aikatan sun bukaci gwamnati da ta sauya batun kayyade farashin mai domin bai wa kowani dan kasuwa daman sayar da shi yadda ya kama, batun da babu shaka zai haifar da tashin mai.

Al'ummar Najeriya dai na ci gaba da kokawa da matsayin firashin mai a kasar wanda ke sake jefa talaka a cikin hali na kunci.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.