Kungiyar Kwadago ta shirya soma yajin aiki
Yan Nigeria sun sa idanu yau laraba domin ganin ko da gaske ne kiran da kungiyar kwadago ta yiwa ma'aikata da a fara yajin aiki zai yi tasiri ganin cewa kotun sasanta rikicin ma'aikata ta nemi a jingine yajin aikin sai nan gaba kadan.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ministan shari’ar kasar Abubakar Malami ne ya shigar da karar a gaban kotu, inda mai shari’a Babatunde Adejumo ya bukaci ma’aikata da su dakatar da shiga yajin aikin sai bayan gudanar da shari’ar a raanr 24 ga wannan wata.
To sai dai jama’a na ci gaba da kintsawa domin kada yajin aikin ya rutsa da harkokinsu.
Bayan ganawar kungiyar da gwamnati dai an kasa cimma matsaya duk da tsawon lokacin da suka shafe don ganin sun fahimci juna akan lamarin wanda ya haifar da cece-kuce a dukkanin fadin Najeriya.
Shugaban kungiyar kwadagon Ayuba Waba ya shaida wa manema labarai cewa, karin farashin man daga Naira 86 zuwa 145 ba shi da wani alfanu, lura da cewa an dauki irin wannan matakin a bangaren wutar lantarki amma duk da haka ba a samu wadatuwar wutar ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu