Isa ga babban shafi
Najeriya

Masarautar Kano ta sauke Lamido daga sarautar Ciroma

Rahotanni daga fadar Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, sun tabbatar da cewa fadar ta tube Alhaji Lamido Ado Bayero daga sarautarsa ta Chiroman Kano, tare da maida sarautar Chiroman ga dan uwansa Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Mai martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi.
Mai martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi.
Talla

Wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ciki har da wakilinmu Abubakar Isah Dandago, mai dauke da sa hannun Galadiman Kano Abbas Sanusi, ta ce matakin ya biyo bayan kin yin muba ya’a ga Sarki Muhammadu Sanusi na biyu da shi toshon Chiroman yayi, tare kuma da kaucewa dukkanin al’amuran masarautar tun bayan nada Sanusi na biyu, wanda hakan ba karamin cin fuska ne ga masarautar ba.

Lamido Ado Bayero dai shi ne babban da ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero, kuma a  baya an yi hasashen zai iya gadon sarautar Kano.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.