Isa ga babban shafi
Nijeriya,kano

An mayar wa Sarki Sunusi fasfo din sa

Hukumar tsaro ta farin kaya SSS a Najeriya, ta mayar wa Sarkin Kano Sanuni Lamido Sanusi na II fasfonsa din sa bayan da aka kwace masa a watan Mayu, lokacin da ya ke takun saka da gwamnatin Goodluck Jonathan.

Sarki Kano Sunusi Lamido Sunusi II
Sarki Kano Sunusi Lamido Sunusi II Sanusiweb
Talla

Babban mai bai wa Gwamnan Kano shawara kan lamurran da suka shafi harakokin masarautar Kano Tijjani Mailafiya ya tabbatarwa manema labarai cewa Jami’an tsaron na farin kaya sun mayar wa Sarkin Kano da fasfo dinsa.

A kano ne flin saukar jirgi na Aminu Kano aka kwace wa Sarki Sanusi Fasfo dinsa lokacin da yake shirin hawa jirgi domin zuwa kasar Saudiya don gudanar da aikin Umrah.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.