Isa ga babban shafi
Najeriya

Ban ki-Moon ya gana da Gwamnonin Najeriya

Rashin tsaro da dai-daito da kuma rabuwar kawunan su ne abubuwa da Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Ban ki-Moon ya mayar da hankali a kai, yayin ganawarsa da Gwamnonin Najeriya a Abuja a ci gaba da ziyarar aiki da ya kai kasar.

Ban Ki-moon lokacin da ya isa birnin Abuja a Najeriya
Ban Ki-moon lokacin da ya isa birnin Abuja a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Duk da dai Ban ya yabawa Kokarin gwamnonin Arewacin kasar, ya na kuma mai cewa akwai bukatar shugabannin su mayar da hankali wajen dakile ayyukan tsaurara ra’ayi.

Ban Ki Moon zai kuma gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari da kuma aje firanni wajen tunawa da ma’aikatan sa da aka kashe lokacin da aka kai harin bam ofishin Majalisar da ke Abuja.

Bayan zantawa da Buhari ana kuma sa ran Ban zai tattauna da Kungiyoyin fararar hula da masu zaman kansu kan raya Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.