Ban Ki-Moon ya isa Najeriya
Sakatare Janar na Majasar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon ya isa Kasar Najeriya a yammacin yau lahadi domin tunawa da ranar da Kungiyar Boko Haram ta kai harin Bam a Ofishin Majalisar dake birnin Abuja shekaru uku da suka gabata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Da misalin karfe hudu agogon Kasar ne, Mr. Ban ya sauka a filin jiragen Sama na Abuja yayin da kuma ake kyautatata zatan cewa zai tabo batun yaki da ta’addanci a tattaunawar da zai yi da Shugaba Muhammadu Buhari.
Kana Mr. Ban zai sanya fure, domin tunawa da cika shekarau 4 da harin wanda ya kashe mutane 21 a wancan lokacin a Ofishin Majalisar.
Tun bayan da Shugaba Buhari ya karbi madafun ikon kasar, ake ci gaba da yakar mayakan na Boko Haram, da kawo yanzu suka hallaka dubun dubatar mutane a kasashen yammacin Afrika da suka hada da Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu