Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Banki Moon zai fara ziyara a Najeriya

Gobe Lahadi ake sa rai sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, zai fara ziyara a Najeriya, don tunawa da ranar da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai wani mummunan harin ta’addanci a Ofishin majalisar ta Dinikin Duniya dake Abuja.

Sakatare Janar na MDD Ban ki-Moon
Sakatare Janar na MDD Ban ki-Moon
Talla

Ban Ki Moon, zai kuma gana da shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari, daya karbi madafun ikon kasar a ranar 29 ga watan Mayu, da ma sauran jami’an majalisar.
Yayin ziyarar, Ban zai aza fure, don cika shekaru 4 da harin da aka yi amfani da wata mota aka ka iwa ginin majalisar hari.
Tuni kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin harin, daya hallaka mutane 21 a wancan lokacin.
Tun bayan da shugaba Buhari yak arbi madafun ikon kasar, ake ci gaba da sasukar mayakan na Boko Haram, da zuwa yanzu suka hallaka dubun dubatar mutane a kasashen yammacin Afrikam da suka hada da Najeriya, Nijar, Kamaru da kuma Chadi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.