Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Najeriya za ta buga wasan Zumunci da Nijar a 8 ga Satumba

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF tace a ranar 8 ga watan Satumba, ‘Yan wasan Super Eagles za su buga wasan sada zumunci da ‘Yan wasan Mena na Nijar a garin Fatakwal na kudancin kasar.

Tambarin hukumar kwallon kafar Najeriya NFF
Tambarin hukumar kwallon kafar Najeriya NFF completesportsnigeria.com
Talla

NFF ta fadi a shafinta na Intanet cewa tana kan tattaunawa da mahukuntan Jihar Rivers domin samun damar buga wasan da Nijar a filin Adokiye Amiesiamaka inda ‘Yan wasan Najeriya ‘yan kasa da shekaru 23 suka doke Congo a wasannin neman shiga gasar cin kofin Afrika ta ‘yan kasa da shekaru 23.

Hukumar kwallon Nijar ta tabbatar da amincewa da buga wasan na sada zumunci da Najeriya a wasikar da ta aika wa Sakatare Janar na Hukumar kwallon kasar Muhammad Sanusi tun a ranar 6 ga watan Agusta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.