Isa ga babban shafi
Najeriya

Wata mata ta kai harin bam a Maiduguri.

A yau talata wata mata ta kai harin kunar bakin wake a wani sansanin soji dake unguwar Sabon gari a Maidugurin jahar Borno dake arewacin Najeriya inda mutane hudu suka rasa rayukan su nan take.

Dan sanda tsaye a wani wurin da aka kai harin bam a Maiduguri.
Dan sanda tsaye a wani wurin da aka kai harin bam a Maiduguri. AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Wannan harin dai ya biyo bayan jerin hare hare da suka auku a sassa daban daban na arewacin kasar a makon da ya gabata inda mutane da dama suka rasa rayukan su.

Al'ummar kasar dai na ci gaba da yin kira ga shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya gaggauta kawo karshen ayyukan Kungiyar Boko Haram da kawo yanzu suka salawantar da rayukan mutane sama da dubu hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.