Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta ce, akwai hujjoji kan laifin da Sojin Najeriya suka aikata.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa, akwai kwararan hujjoji da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC za ta iya amfani da su wajan tuhuman manyan dakarun Najeriya da ake zargi da aikata laifukukan yaki a lokacin fafatawa da Boko Haram  

Dakarun tsaro a birnin Maiduguri dake jihar Borno a Najeriya.
Dakarun tsaro a birnin Maiduguri dake jihar Borno a Najeriya. REUTERS/Stringer
Talla

A wani rahoto da kungiyar Amnesty Internaional ta fitar mai shafuka 133 ta zargi manyan jami’an sojin Najeriya biyar da cin zarafin bil-adama da aikata laifukan yaki a lokacin yaki da Kungiyar ta Boko Haram dake tada kayar baya a arewa laso gabashin Najeriya.

A cewar Amnesty international, sai da ta gudanar da bincike da ya hada da hirarraki da dumbin jama’a dama majiyoyin sojin kasar ta kafin ta fitar da rahoton.

Zarge zargen dai da ake yiwa manyan jami’an sojin sun hada da kisan mutane sama da 1,200 ba gaira ba dalili da dakarun Najeriya suka yi, yayin da a bangare guda kuma, ake zarginsu da laifin tsare matasa dubu 20 a lokacin yaki da yan Boko haram.

Sakatere Janar na Amnesty international, Salil Shetty, ya bayyana cewa hujjojin da suka tattaara kan wannan batun sun kai matuka wajan tayar da hankula.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.