Isa ga babban shafi
MDD

Mutane miliyan 36 sun kauracewa gidajensu saboda rikici

Wani rahoto da aka fitar ya bayyana cewa Rikici da yake-yake a kasashen irinsu Syria da Ukraine da kuma rikicin Boko Haram a Najeriya ya sa mutane kimanin Miliyan 38 sun kauracewa gidajensu. Wannan adadin kuma ya yi daidai da adadin yawan mutanen da ke biranen New York da London da Beijing.

'Yan gudun Hijirar Syria a  Lebanon
'Yan gudun Hijirar Syria a Lebanon Reuters/Jamal Saidi
Talla

Rahoton wanda Kungiyar da ke sa ido game da sha’anin ‘yan gudun hijira ta fitar a ranar Laraba ya bayyana cewa kimanin mutane miliyan 38 ne suka kauracewa gidajensu a kasashen da ake rikici irin su Syria da Ukraine da Iraqi da Najeriya.

Rahoton ya ce a bara akwai adadin mutane Miliyan 11 da suka kauracewa gidajensu.
A cikin rahoton kuma an kiyasta cewa kimanin mutane dubu Talatin ke barin gidajensu saboda rikici a kowace rana.

Rahoton hukumar ta IDMC ya bayyana cewa wannan shi ne adadi mafi muni, wanda ke nuna gazawa daga bangaren hukumomi wajen kare rayukan fararen hula.

Kasar Iraqi ce ke da yawan mutanen da suka kauracewa gidajensu saboda rikicin mayakan IS da ke da’awar jihadi a kasar, sai kasar Syria da kuma kasar Ukraine da ke fama da barazanar ‘Yan tawaye da kuma mutanen Najeriya da ke fama da matsalar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.