Isa ga babban shafi
Najeriya

Wata cuta mai saurin kisa ta bulla a kudancin Najeriya

A Nigeria, wata cuta da har yanzu ba a gano taba, tayi sanadiyyar rasa ran mutane 17, a wani gari mai suna Ode-Irele dake jihar Ondo. Jami’an gwamnatin jihar sun ce cutar, da ta bulla yanki a farkon wannan mako, na hallaka mutum cikin sa’oi 24 da kamuwa. Mai magana da yawun gwamnatin jihar ta Ondo Kayode Akinmade ya shaida wa kamfanin dillancin labarum Faransa na AFP cewa, alamun cutar sun hada da ciwon kai, rama, gani dushi dushi da gushewar hankali.Sai dai ya kara da cewa cutar bata da alaka da Ebola mai saurin yaduwa. 

Wasu jami'an kula da lafiya
Wasu jami'an kula da lafiya Online
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.